Malaga ta sayi Van Nistelrooy daga Hamburg

nistelrooy
Image caption Ruud Van Nistelrooy

Kungiyar Malaga ta Spain ta kulla yarjejeniya da gogaggen dan wasan Holland Ruud van Nistelrooy daga Hamburg.

Dan kwallon wanda zai cika shekaru 35 a ranar daya ga watan Yuli, a ranar Alhamis ne aka gabatar dashi gaban magoya bayan kulob din.

Malaga bata bada wani karin bayani ba akan batun sabon dan kwallon.

Kafafen yada labarai a Spain sunce an gwada lafiyar van Nistelrooy kuma ya sanya hannu a kwangilar shekara guda tare da zabin sabunta kwangilar.

Malaga ce dai ta goma sha daya akan teburin La Liga ta Spain a kakar wasa data wuce.

Van Nistelrooy ya koma Hamburg ne a watan Junairun 2010 bayan shafe shekaru hudu a Real Madrid.

A baya dai dan wasan ya taka leda a PSV Eindhoven da Manchester United.