Brad Friedel ya koma Tottenham

Brad Friedel
Image caption Tottenham na da kwararrun gololi uku ke nan

Golan Aston Villa, kuma dan kasar Amurka Brad Friedel ya koma Tottenham, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu.

Dan wasan mai shekaru 40 da haihuwa, a karshen watannan ne kwantiraginsa za ta kare a Aston Villa.

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce : "Abu ne mai kyau ka samu gololi guda uku kwararru a kulob dinka.

"Hakan na nuna cewa za a dinga kokawar neman wuri, musamman ganin adadin wasannin da za mu buga badi."

Friedel, wanda ba zai sa Spurs ta kashe wasu kudade ba, yana da kwarewa sosai a Premier bayan da ya zo Liverpool a 1997 daga Columbus Crew na Amurka.