Zan yi maraba da Hughes ko Hiddink - Terry

John Terry Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption John Terry shi ne kyaftin din Chelsea da kuma Ingila

Kyaftin din Chelsea John Terry ya ce zai yi maraba da nadin Mark Hughes ko Guss Hiddink a matsayin sabon kocin kulob din.

Kulob din na neman wanda zai maye gurbin Carlo Ancelotti ne bayan da aka kori dan kasar ta Italiya a karshen kakar da ta gabata.

Hughes, wanda ya yi murabus daga Fulham ranar Alhamis, da kuma kocin Turkiyya Hiddink, ana danganta su da mukamin.

Hiddink ya taba zama kocin wucin gadi a Chelsea a shekara ta 2009, inda ya lashe kofin FA, yayin da shi kuma Hughes tsohon dan wasan Chelsea ne.

"Ana ta rudani yanzu kan mukamin," a cewar Terry wanda ke magana a lokacin da Ingila ke shirin fafatawa da Switzerland ranar Asabar a gasar share fagen shiga gasar kasashen Turai.

"Na yi bakin ciki da tafiyar Carlo, kuma a matsayinmu na 'yan wasa muna jiran hukuncin da shugabannin kulob din za su dauka game da sabon kocin. A kwai mutane da dama da ake alakantawa da aikin."