Ancelotti zai tafi hutun shekara guda

Image caption Chelsea ta sallami Ancelotti, bayan da aka kammala kakar wasan bana

Tsohon kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce zai dau hutun shekara guda domin ya huta daga al'amuran kwallon kafa.

Kocin mai shekarun haihuwa 51, ya shaidawa wata Jarida a Italiya cewa: "Bana cikin hanzarin komawa harkar kwallon kafa. Ina ganin bai kamata inyi hakan ba.

"Babu kungiyar da ta tuntube ni a Ingila kuma banyi magana da kowa ba a Roma. Duk jita jita ne."

Matakin da Ancelotti ya dauka na kin horon wata kungiya na tsawon shekara guda, ya sanya Aston Villa cikin rudu, saboda rahotanni na nuni da cewa kungiyar na neman ya jagoran ce ta.

Akwai rahotanin ma dake nuni da cewa Ancelotti na iya komawa kungiyar Fulham ko Queen's Park Rangers ko kuma kungiyar Roma da ke Italiya.