'Bharain ta shiryawa gasar Grand Prix'

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Hukumar FIA ta ce Bharain ta shiryawa gasar tsaf

Hukumar kula da tseren motoci ta Grand Prix ta ce komai ya daidaita a yanzu a kasar Bahrain domin komawa gasar a can.

Kasar ta Bahrain ce dai ke daukar bakuncin gasar tun shekarar 2004.

An zartar da komawa gudanar da gasar ne bayan hukumar kula da gasar FIA ta ce al'amura sun daidaita a yanzu a kasar.

Shugaban hukumar Jean Todt ya shaida wa BBC cewa, hukumar ta aike da daya daga cikin mataimakan shugaban kungiyar zauwa kasar ta Bahrain wadda ta yi fama da rikici a baya, kuma ya kawo rahoton cewa al'amura sun daidaita a kasar.

A da dai an shirya gudanar da gasar ne a ran 13 ga watar Maris da ya gabata, sai dai an dakatae a watan Fabrairu sakamakon zanga-zangar neman kafa tsarin demokradiyyar da aka yi a kasar.

Zanga-zangar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da ashirin.

A yanzu za a gudanar da gasar ne a ranar 30 ga watan Oktoba mai zuwa.

Sai dai wata kungiya mai suna Avaaz, ta musanat rahoton cewa al'amura sun daidaita a kasar ta Bahrain.

Daraktan kungiyar Alex Wilks ya ce, a cikin mako dayan da ya gabata, 'yan sanda sun ci gaba da amfani da hayaki maisa hawaye, da harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma raunata mutane da dama.