Rio Ferdinand ya jinjinawa Nasri

Rio Ferdinand
Image caption Rio Ferdinand ya ce Nasri na daga cikin 'yan wasan da suka fi kwarewa

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand, ya yabawa kwarewar dan wasan Arsenal Samir Nasri a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa Man United na nemansa. Ana danganta Nasri da tafiya Manchester United, bayan da tattaunawa kan kwantiraginsa a Arsenal ta ci tura, sannan kuma dan wasan bai kawar da yiwuwar barin kungiyar ba.

Bayan da Paul Scholes ya yi ritaya a makon da ya gabata, rahotanni sun ce Sir Alex Ferguson na neman Nasri domin ya mayer gurbin Scholes.

Gidan talabijin na Sky ya ambato Ferdinand na cewa: "Samir Nasri gogaggen dan wasa ne."

"Dan wasa ne mai hazaka sosai, kuma yana zira kwallaye aka-akai.

"A gani na yana daya daga cikin 'yan wasan da suka fi kwarewa a yanzu.

"Faransa ta saba haifar da kwararrun 'yan wasa a gasar Premier. Thierry Henry ya taka leda sosai. Haka ma Cantona, kada kuma mu manta da Marcel Desailly."