Iran ta soki FIFA da yin mulkin mallaka

Fifa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A 'yan kwanakin nan FIFA ta shiga cikin rudani da dama

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad ya soki Hukumaer kwallon kafa ta FIFA ta yin mulkin mallaka, bayan da aka hana tawagar kwallon matan kasar sanya dan kwali.

Jakadan kasar a Jordan Mustafa Musleh Zadeh, ya ce matakin ya sabawa halayyar dan adam kuma siyasa ce kawai.

Kalaman na Ahmadinejad su ne mafiya girma tun bayan da kasar ta fasa buga wasan share fagen shiga gasar Olympic da Jordan ranar Juma'a, saboda ba za su buga wasan ba tare da sun rufe jikinsu ba.

"Wannan kama karya ce daga 'yan mulkin mallaka da ke son kakabawa jama'a yanayin rayuwarsu da suke yi, kamar yadda ya fada a wajen taron manema labaran da yake yi shekara-shekara.

"Za mu yi duk mai yiwuwa wajen kwato yancin yaranmu."

Zadeh ya ce Iran za ta yi korafi zuwa Hukumar kula da Kwallon kafa ta Asia.

Ita dai FIFA ta ce ta dauki matakin hana matan Iran din rufe cinyarsu da kuma gashinsu ne domin kariya.