Liverpool na gab da sayen Henderson

Jordan Henderson
Image caption Dan wasan mai shekaru 20 zai je Liverpool domin a gwada lafiyarsa

Liverpool da Sunderland sun cimma matsaya kan farashin fan miliyan 20 domin sayar da dan wasan tsakiya na Sunderland Jordan Henderson.

Dan wasan na Ingila mai shekaru 20 zai yi tattaki zuwa Liverpool domin a gwada lafiyarsa kuma ya tattauna tsakaninsa da su.

Wata sanarwa da Sunderland ta fitar ta ce: "Mun amince da farashi kan sayar da Jordan Henderson ga Liverpool, kuma zai je Anfield tare da goyon bayanmu."

A baya Sunderland ta yi watsi da tayin Liverpool, wanda akai hasashen ya kai fan miliyan 16.

Liverpool na fatan za a kammala cinikin kafin Henderson ya hade da tawagar 'yan kasa da shekaru 21 na Ingila ranar Laraba domin gasar cin kofin kasashen Turai.

Ana saran dan wasan gaba na Liverpool David Ngog, mai shekaru 22, zai koma Sunderland a wani bangare na cinikin, amma har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.