An baiwa Martinez damar tattaunawa da Villa

Roberto Martinez
Image caption Roberto Martinez ya taka rawar gani a Wigan

Wigan ta baiwa kociyanta Roberto Martinez damar tattaunawa da Aston Villa kan yiwuwar komawarsa kulob din.

Tsohon kocin na Swansea shi ne ake saran zai gaji Gerard Houllier, wanda ya bar Aston Villa a wannan watan sakamakon ciwon zuciyar da yake fama da shi.

Shugaban Wigan Dave Whelan ya shaidawa jaridar Daily Telegraph, cewa ya baiwa Martinez damar amma ya kara da cewa "zai yi mamaki" idan Martinez ya bar kulob din.

Tuni dai aka fitar da tsammani kan Steve McClaren da Rafael Benitez da Mark Hughes.

Kuma ganin ficewar wadannan manyan kociyoyi uku, abu ne mai yiwuwa Martinez ya zamo sabon kocin na Aston Villa.