Ashley Young zai gana da shugaban Villa

Image caption Ashley Young

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Aston Villa, Ashley Young, zai gana da shugaban kulob din Randy Lerner domin tattaunawa a kan makomar sa, bayan ya bayyana cewa yana son likkafar sa ta yi gaba.

Akwai bayanan da ke nuna cewa dan wasan na son komawa Manchester United ko Liverpool.

Ashley Young na da sauran shekara daya a kwantiragin da ya sanya wa hannu da kulob din Aston Villa, sai dai ya ce yana son ya samu kwarewar bugawa a gasar cin kofin zakaru ta nahiyar Turai da ma sauran gasanni na duiya.

Kwallon da dan wasan ya fanshe wa kasar sa ta Ingila a kunnen dokin da suka buga da kasar Switzerland ya kara masa tagomashi.

Dan wasan ya kara da cewa, a wata mai zuwa zai cika shekaru ashirin da shida a duniya, don haka yanzu yake ganiyar sa ta buga kwallo.