Martin Jol ne sabon kocin Fulham

Image caption Martin Jol

Kungiyar Fulham dake Ingila ta nada Martin Jol a matsayin sabon mai horadda kungiyar, bayan da Mark Hughes ya yi murabus a makon daya gabata.

Jol wanda ya taba horon kungiyar Tottenham da Ajax a baya, zai jagoranci kungiyar Fulham ne na tsawon shekaru biyu kuma akwai yiwuwar a kara mishi shekara guda, idan ya taka rawar gani.

Jol ya ce: "Ina matukar farin cikin, da wannan dama da aka bani. Fulham babbar kungiya ce, da keda dimbin magoya baya."

Hughes ya yi murabus ne daga Fulham a ranar biyu ga watan Yuni, bayan shekara guda da fara horon kungiyar.