Phil Jones na shirin komawa Manchester United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Phil Jones ya takawa Blackburn leda sau 40.

Rahotanni sun ce dan wasan bayan Blackburn Phil Jones na shirin komawa kungiyar Manchester United a kudi fam miliyan 17.

A yanzu haka dai ana duba lafiyar dan wasan, wanda ke takawa tawagar Ingila 'yan kasa da shekaru 21 leda.

Jones dai ya fara taka leda ne a gasar Premier a watan Mayun bara, inda kuma ya taka rawar gani.

Jones dai na iya fuskantar matsala wajen samun taka leda a karo na farko, saboda kwararrun 'yan wasan bayan da Manchester United take dasu kamar su Rio Ferdinand da Nemanja Vidic da Chris Smalling da kuma Jonny Evans.