An yi sulhu tsakanin Apple da Nokia

An yi sulhu tsakanin Apple da Nokia Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Nokia da Apple ne kan gaba a fagen samar da wayoyin salula

Biyu daga cikin manyan kamfanonin fasahar kyara-kyare na duniya wato Apple da kuma Nokia, sun cimma matsaya kan rikicin da ya dabaibayesu.

Kamfanin Apple na Amurka ya amince ya biya kamfanin Nokia na kasar Finland wasu kudade game da amfani da fasahar sa da ya yi wajen kyara wasu wayoyin salula.

Nokia ta kai karar kamfanin na Amurka kan keta hakkin fasaharta a shekara ta 2009 - daga nan sai Apple ita ma ta kai karar Nokia.

Kamfanin Nokia shi ne na daya wajen kyara wayar salula a duniya, amma Apple ya mamaye fagen samar da manyan wayoyi.

Apple ya fada a wata sanarwa cewa fasahar da ake magana a kai bata shafi yawancin fasahar da yake amfani da ita a shahararriyar wayarsa ta iPhone ba.

Nokia ta ce kudaden da ba a bayyana adadinsu ba, za su yi tasiri mai kyau kan ribar da za ta samu a watanni uku masu zuwa wacce aka yi hasashen za ta yi kasa.