Arsenal na shirin sayen sabbin 'yan wasa

Arsenal na shirin sayen sabbin 'yan wasa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da Arsenal ta dauki wani kofi tun FA Cup na shekara ta 2005

Shugaban Arsenal Ivan Gazidis ya yi hasashen cewa za a yi rububin sayen 'yan wasa a kakar bana, a daidai lokacin da kulob din ke kokarin sayo sabbin 'yan wasa.

Rabon da Arsenal ta dauki wani kofi tun FA Cup na shekara ta 2005, yayin da suka gaza a bara bayanda ta nuna cewa za su lashe kofuna da dama. "Gaskiya ne mun fuskanci koma baya kuma a bana za mu ga tururuwar 'yan wasa," a cewar Gazidis lokacin da yake magana da magoya bayan kulob din.

Ya kara da cewa: "Da farko mun fara kamar gaske kamar za mu lashe dukkan kofunan, amma daga bisani sai muka koma gidan jiya."

"Nima ina jin irin takaicin da kuke ji.

"Babu shakka sabbin 'yan wasa za su zo, kuma wasu daga cikin tsaffin na mu za su tafi, kamar yadda Arsene Wenger ya fada a baya."

A yanzu dai Arsenal sun sayi Carl Jenkinson daga Charlton, sai dai ana sukar Wenger da rashin sayen kwararrun 'yan wasa.