Zagayen rukuni na gasar Confederation Cup

JS Kabylie
Image caption JS Kabylie sun taba lashe gasar zakarun Afrika

Kungiyar Asec Mimomas ta Ivory Coast da InterClube na daga cikin kulob na farko da suka fara samun gurbi a zagayen rukuni na gasar cin kofin Caf Confederation Cup.

InterClube ta tashi biyu da biyu a wasanta da Difaa el-Jadida na Morocco, amma duk da haka ta samu ta kai bantanta.

Tsaffin zakarun Afrika Asec sun yi kunnen doki ne da Primeiro na kasar Angola inda suka lashe wasanni biyun da ci 5-1.

Moghreb Fes na Morocco ma sun tsallake zuwa zagayen rukunin bayan da suka doke Zesco United na Zambia da ci 2-0.

Wankin hula ya so ya kai JS Kabylie na Algeria dare, wadanda a baya suka taba lashe gasar zakarun Afrika, amma sun samu sun lashe Diaraf na Senegal da ci 2-0 a Tizi-Ouzou bayanda aka tashi babu ci a wasan farko.

Club Africain na Tunisia sun tsallake duk da kashin da suka sha a hannun Sofapaka na Kenya da ci 3-1, sakamakon nasarar da suka samu a wasan farko da ci 3-0.