Raymond Domenech na son komawa Algeria

Raymond Domenech
Image caption A hannun Domenech aka samu rudani a tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya a 2010

Tsohon kocin Faransa Raymond Domenech ya ce a shirye yake ya karbi jagorancin kasar Algeria bayanda aka nemi shi da ya maye gurbin kocin kasar.

Tsohon kocin Ivory Coast Vahid Halilhozdic, shi ma ya ce yana neman zamowa kocin kasar ta Algeria.

Kocin kasar Abdelhak Benchikha wanda dan Algeria ne, ya yi murabus bayan da Morocco ta doke su a farkon watan nan a birnin Casablanca.

Wakilan Domenech, Laminak Conseil agency, sun fada a wata sanarwa cewa Hukumar kwallon kafa ta Algeria ta nemi kocin. "An nemi Domenech domin yiwuwar zamowa sabon kocin kasar Algeria," kamar yadda sanarwar da bayyana.

A hannun Domenech aka samu rudani a tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya a 2010, inda 'yan wasan suka yi yajin aiki.