Nottingham Forest ta nada McClaren a matsayin koci

Steve McClaren
Image caption Steve McClaren ya yi aiki a kungiyoyi da dama

Nottingham Forest ta nada tsohon kocin Ingila Steve McClaren a matsayin koci, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru uku.

Kocin dan shekaru 50 da haihuwa ya maye gurbin Billy Davies, wanda aka kora a ranar Lahadi.

Kulob na karshe da McClaren ya jagoranta a Ingila su ne Middlesbrough, sannan kuma ya yi aiki tare da FC Twente na Holland da kuma Wolfsburg na Jamus.

"Steve yana da kwarewa sosai a harkar koci a matakin kulob," a cewar shugaban kulob din Mark Arthur.

"Kulob din ya yi wuf wajen daukarsa saboda abu ne mai wahalar gaske ka samu koci mai kwarewarsa ba tare da yana aiki a wata kungiya ba."

Za a gabatar da McClaren a hukumance a ranar Alhamis.

Nadin na sa ya zo ne bayanda Davies ya kasa kai kulob din ga gaci a wasan kifa daya kwala na shiga gasar Premier a karo na biyu a jere.