Rangers za ta fara tattaunawa kan Hemed

Tomer Hemed Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tomer Hemed ya haskaka sosai a Macabbi Haifa

Rangers za ta fara tattaunawa da wakilan Tomer Hemed dan kasar Isra'ila, game da yiwuwar komawarsa kulob din.

Dan wasan mai shekaru 24, kwantiraginsa za ta kare da Macabbi Haifa a karshen watan Juni.

Hemed ne ya fi kowanne dan wasa zira kwallaye a Macabbi Haifa a kakar wasannin bara, inda ya zira kwallaye 17.

Ya kuma buga wasansa na farko ga kasar Isra'ila a farkon watan nan.

Da shi aka fara wasan Isra'ila da Latvia a makon da ya gabata, inda ya taimaka wa Yossi Benayoun ya zira kwallo daya a nasarar da suka samu da ci 2-1.

Akwai kulob-kulob da dama a Italiya da Spaniya da Belgium da ke neman dan wasan, amma batun buga gasar zakarun Turai ka iya baiwa Rangers dama kan sauran.

Akwai bayanan da ke nuna cewa Hemed ya tattauna da Beram Kayal na Celtic, tsohon dan wasan Maccabi, kan yiwuwar komawarsa Glasgow.