ACN 2013: Har yanzu Libya muka sani - CAF

CAF
Image caption Caf na taka-tsantsan kafin daukar mataki a kan Libya

Hukumar kwallon kafa ta Afrika (caf), ta ce har yanzu Libya ta sani a matsayin kasar da za ta dauki bakuncin gasar kasashen Afrika a 2013, amma tana lura da lamuran da ke faruwa a can.

Sai dai Caf ta ce tana da shirin ko ta kwana a kasa ganin irin rikicin da ake yi a kasar ta Libya.

'Yan tawayen da ke kokarin kawar da shugaba Gaddafi na Libya, su ke rike da akasarin Gabashin kasar.

"Ba shakka muna baiwa abubuwan da ke faruwa a can kula wa ta musamman," kamar yadda Sakataren Caf Hicham El Amrani ya shaidawa BBC.

"Dukkan wasannin da Libya za ta dauki bakunci ba wai kawai na gasar cin kofin kasashen Afrika ba, har ya zuwa yau din nan suna nan kamar yadda aka tsara.

"A lokaci guda kuma kwamitin zartarwa na Caf na da shirin ko ta kwana".