Martinez ya fasa komawa Aston Villa

Roberto Martinez
Image caption Abaya an yi hasashen Martinez zai koma Aston Villa

Kocin Wigan Roberto Martinez ya yanke shawarar ci gaba da zama a Wigan bayanda Aston Villa ta yi kokarin daukarsa.

Martinez, dan shekaru 37, zai kara sanya hannu a kan kwantiragin shekaru uku maimakon komawa Villa.

"Roberto ya gana da shugaban Wigan a farkon makon nan kuma ya yanke shawarar girmama kwantiraginsa," a cewar sanarwar Villa.

Whelan ya ce yana da kwarin gwiwa tsohon kocin na Swansea Martinez zai ci gaba da zama a Wigan duk da cewa ya bashi damar tattaunawa da Villa, kuma hakan ya tabbata.

"Kudi ba su ne matsalar Martinez ba", a cewar Whelan. "Villa ba za su ji dadi ba, amma ni ina farin ciki.