Boateng ya kusa komawa Bayern Munich daga City

boateng Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jeroma Boateng

Dan kwallon Manchester City Jerome Boateng ya amince da kwangilar shekaru hudu a Bayern Munich amma dai sai City din ta amince.

Dan wasan mai shekaru 22 ya koma City ne daga Hamburg a shekara ta 2010.

Yace"da gaske na amince da yarjejeniyar shekaru hudu da Bayern, yanzu ya rage ga City ta yarda".

Bayan nasarar daya samu a gasar cin kofin duniya tare da Jamus a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010, Boateng ya koma City amma sau 24 kawai ya bugawa tawagar kwallo.

Boateng na bugawa City a baya ta bangaren dama, amma yafi son ya buga ta tsakiya.