Arsenal na tattaunawa da Lille akan Gervinho

gervinho
Image caption Gervinho

Kungiyar Lille ta Faransa na shirin tattaunawa da Arsenal akan batun sayarda dan kwallon Ivory Coast Gervinho.

Dan kwallon mai shekaru 24 ya zira kwallaye 15 inda ya taimakawa Lille ta lashe gasar Faransa da kuma na kofin kalubale a kakar wasan data wuce.

Janar Manajan Lille Frederic Paquet yace" yanason ya tafi kuma ya ganawa da Arsenal".

Paris St Germain itama ta nuna kwadayin sayen Gervinho amma dai Paquet baya son ya sayarwa wata kungiya da take Faransa.

Sai dai Paquet ya kuma bayyana dan wasanshi mai shekaru 20 Eden Hazard a matsayin dan kwallon da ba zasu sayar ba.