Kwamitin da'a na Fifa ya yiwa Blazer tambayoyi

blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blazer na hannun damar Blatter ne

Kwamitin da'a na Fifa ya yiwa Sakatare Janar na hukumar Concacaf Chuck Blazer tambayoyi bayan kungiyoyin yankin Caribbean sun yi korafi akanshi.

Blazer ne ya tona asiri har aka soma binciken daya janyo akan dakatar da manyan jami'an Fifa biyu Jack Warner da Mohamed Bin Hammam akan zargin cin hanci da rashawa.

Korafin nada alaka da yadda Blazer yayi zargin a taron Fifa a Zurich a watan Mayu.

Blazer yace"bani da damuwa za a warware matsalar cikin ruwan sanyi".

Shugabanni kungiyoyin kwallon kafa 11 daga yankin Caribbean ne suka rubuta takardar koken akansa.

Blazer yayi zargin cewar Jack Warner da Bin Hammam sun biya wakilan yankin Caribbean dala dubu arba'in kowanne don su zabi Bin Hammam a matsayin shugaban Fifa.