Kim Clijsters ta fasa shiga Wimbledon open

clijsters
Image caption Kim Clijsters

'Yar wasan tennis ta biyu a duniya Kim Clijsters ta fasa shiga gasar Wimbledon open a mako mai zuwa saboda rauni a kafarta.

'Yar shekaru ashirin da takwas ta jimu a gasar Unicef Open a Netherlands a ranar Talata.

Tace"a wannan lokacin ina cikin damuwa akan abinda ya faru".

'Yar tennis ta farko a duniya Caroline Wozniaki da Vera Zvonareva da Li Na third da Victoria Azarenka dali da kuma Maria Sharapova duk zasu fafata a gasar.

Clijsters a shekara ta 2007 tayi ritaya da tennis sannan shekaru biyu bayan ta haifi 'ya mac sai ta dawo kuma ta lashe gasar US Open sannan ta lashe gasar Australian Open a bana.