Abin takaici ne ace zamu sayarda Gyan-Quinn

gyan
Image caption Asamoah Gyan

Shugaban kungiyar Sunderland Niall Quinn ya bayyana rahotannin dake cewa zasu sayarda Asamoah Gyan a matsayin abin takaici.

An bada rahoton cewar dan kwallon mai shekaru 25 an sashi a kasuwa a Sunderland.

Quinn yace"wannan labarin abin takaici ne kuma anason a janyo mana matsala a 'yan wasanmu". Gyan ya koma Sunderland ne a watan Agustan 2010 akan fiye da fan miliyan 13 daga kungiyar Rennes ta Faransa kuma ya zira kwallaye 11 a kakar wasa ta farko a kulob din.

Sunderland a farkon wannan watan ta sayarwa da Liverpool Jordan Henderson akan fan miliyan 20.

Sai dai a halin yanzu ana alakanta Sunderland da siyo dan Koriya ta Kudu Ji Dong-Won da kuma dan Liverpool David Ngog.