Shearer ba zai jagoranci Cardiff ba

Alan Shearer
Image caption Alan Shearer ya taba zama kocin Newcastle

Tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya ce ba zai jagoranci Cardiff City a matsayin koci ba bayan da tattaunawa tsakaninsa da kulob din bata haifar da nasara ba.

Tsohon kocin na Newcastle ya fada a wata sanarwa cewa: "Zan tabbatar cewa ina daya daga cikin mutanen da aka tuntuba da wannan aiki.

"Na yaba da kwazo da kuma manufar shugaban kulob din Dato Chan Tien Ghee a tattaunawar da muka yi.

"Sai dai tattaunawar ba ta yi nasara ba a wannan lokaci".

Tsohon dan wasan na Ingila ya kara da cewa: "Cardiff City babban kulob ne kuma ina yi musu fatan alheri a kakar wasa mai zuwa".

Aikin koci daya tilo da Shearer ya taba yi a rayuwarsa shi ne lokacin da ya jagoranci Newcastle a karshen kakar 2008 - 2009.