Bebe zai koma Besiktas a matsayin aro

bebe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bebe ya koma United a 2010

Dan kwallon Manchester United Bebe ya amince da komawa kungiyar Besiktas ta Turkiya a matsayin aro na shekara guda.

Dan kasar Portugal don ya koma Old Trafford daga Vitoria de Guimaraes a watan Agustan 2010 akan kusan fan miliyan bakwai da rabi, amma baya samun damar taka leda sosai.

Dan kwallon mai shekaru ashirin ya bugawa United ne a wasanni bakwai kacal a kakar wasan data wuce inda ya zira kwallaye biyu.

Kungiyar Besiktas ce ta gama a matsayin ta biyar a kakar wasan 2010/11 a Turkiya.

Bebe ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da United a watan Yulin 2010.

A shekara ta 2009 Bebe mazaunin yankin Casa do Gaiato ne a Portugal inda yake cikin wata kungiya da take taimakawa marasa galihu daina zaman banza.

Komawarsa Old Trafford ta kasance wani babban lamari ganin cewar yaro ne daya taso akan titi.