Fifa ta baiwa Japan gudunmuwar dala miliyan 6

shalkwatar Fifa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shalkwatar Fifa

FIFA ta baiwa hukumar kwallon Japan gudunmuwar dala miliyan shida don taimakawa hukumar farfadowa daga girgizar kasa da kuma guguwar tsunami da suka faru a ranar 11 ga watan Maris.

A cewar shugaban hukumar kwallon Japan Junji Ogura za ayi amfani da dala miliyan hudu da rabi daga cikin kudin wajen taimakawa kungiyar Kashima Antlers don ta gyara filin wasanta da wajajen horon da girgizar kasa ta lalata.

Sannan kuma ayi amfani da dala miliyan daya da rabi wajen gyara filayen wasan da guguwar tafi tsanani.

Har wa yau Fifa ta bada gudunmuwar kwallaye da riguna da takalman kwallo da darajarsu takai dala dubu dari biyar ga wasu yara dubu goma sha biyar ta hannun Adidas.

Dama dai Ogura ne ya bukaci Fifa ta basu agaji lokacin da Sepp Blatter yakai ziyara Japan a watan Mayu.

Haka zalika itama hukumar kwallon Japan ta bada gudunmuwar dala miliyan biyu da rabi ga yankunan da bala'in ya shafa.