Darajar Fabregas ta fadi - In ji Barcelona

Cesc Fabregas
Image caption Cesc Fabregas ana sanya masa rigar Barcelona

Shugaban Barcelona Sandro Rosell ya ce ya yi amannar cewa darajar kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ta yi kasa tun karshen kakar wasanni ta bara.

Kungiyar Barcelona ta yi yunkurin sayen dan wasan mai shekaru 24 a bara.

"Idan mun taya shi fan miliyan 35 bara, tun lokacin an ta cece-kuce, kuma yanzu darajarsa ta fadi," a cewar Rosell.

"Ban son abinda zai faru ba, amma koda za mu saye shi, to ba za mu biya kudi sama da kima ba."

Fabregas ya zo Gunners ne tun shekara ta 2003, amma an dauki hotonsa yana sanye da rigar Barcelona bara tare da 'yan wasan kasar Spain bayan da Spain ta lashe gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

"Ba na zaton zai koma wani kulob a Spain".

"Cesc dan wasan Barca ne, kuma idan da ni shugaban wani kulob ne, da ba zan saye shi ba, tun da ya sanya rigar Barcelona.

Fabregas wanda ya taba yin horo a Barcelona lokacin yana yaro, a 'yan kwanakin da suka wuce ya ce yana jin dadin zamansa a Arsenal.