Premier 2011/2012: Man United za ta kara da West Brom

Premier 2011/2012: Man United za ta kara da West Brom Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manchester United ne suka lashe gasar ta bara

Manchester United za ta yi tattaki zuwa West Brom a ranar Asabar 13 ga watan Agusta domin fara kare kanbunta a wasan farko na gasar Premier ta kakar 2011/2012.

Arsenal za ta fara ne da tattaki domin kece raini da Newcastle, yayin da Chelsea, wacce ta zo na biyu a kakar da aka kammala, za ta kara da Stoke, sai kuma Liverpool da za ta karbi bakuncin Sunderland.

Wasan farko na Premier da Swansea za ta yi, shi ne tsakaninta da Manchester City, yayin da QPR za ta karbi bakuncin Bolton.

Norwich wacce ta dawo Premier bayan shafe shekaru shida ba a yi da ita, za ta kara da Wigan.

A sauran wasannin na ranar farko, Tottenham za ta kara da Everton a filin wasa na White Hart Lane, sai Fulham da Aston Villa a filin wasa na Craven Cottage, yayin da Blackburn za ta karbi bakuncin Wolves.

Bayan ta kara da West Brom a wasan farko, Manchester United za ta fafata da Tottenham, kafin ta kara da Arsenal a wasa na uku.