Bama son Modric ya bar Spurs-Redknapp

modric Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Luka Modric

Kocin Tottenham Hotspur Harry Redknapp ya ce yanasaran zai shawo kan dan wasanshi Luka Modric don ya cigaba da kasancewa da Spurs.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da biyar ya zaku ya koma Chelsea, wacce ta bada tayin fan miliyan 22 akansa.

Redknapp ya shaidawa BBC:"Yaga alamun samun damar buga gasar zakarun Turai kuma muma munason haka".

Spurs ta buga gasar zakarun Turai a karon farko a kakar wasan data wuce amma sai tayi batan dabo sakamakon kasancewa ta biyar a gasar premier ta Ingila.

Sai dai Modric dan kasar Croatia ya bayyana cewar ya bukatar barin kulob din amma yanason ya cigaba da taka leda a London.