Kocin Porto Villa-Boas zai koma Chelsea

villa boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Villa-Boas

Kocin FC Porto Andre Villas-Boas na gabda komawa Chelsea sakamakon korar Carlo Ancelotti a watan Mayu.

Dan shekaru talatin da uku Villas-Boas ya jagoranci Porto ta lashe gasar Europa a kakar wasan data wuce.

Kwangilar kocin a FC Porto ta amince ya koma wani kulob din idan har aka bada pan miliyan 13 da dubu dari biyu.

Sanarwar da Porto ta fitar ta ce bata samu wani tayi ba akan kocin ba.

Amma dai shugaban Porto,Pinto da Costa ya ce kulob din ba zai hana Villas-Boas tafiya ba idan har aka bada kudaden da suka dace.

Costa yace"Villas-Boas nada wani sashi a kwangilarsa na Euro miliyan 15 kuma duk wanda ya biya zamu bar kocin ya tafi".

FC Porto ta lashe kofin uku a kakar wasan data wuce karkashin Villas-Boas a kakar wasan data wuce.

Guus Hiddink ma nada daga cikin wadanda ake ganin zai koma Chelsea,bayan ya lashe kofin FA a matsayin kocin riko a shekara ta 2009.

Villas-Boas wanda ke iya magana da turanci, yayi aiki a karkashin Mourinho a Chelsea da Inter Milan.