Jack Warner ya ajiye mukaminshi a FIFA

warner Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jack Warner

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Jack Warner ya yi murabus daga mukaminsa.

Sanarwar da Fifa ta fitar ta ce “sakamakon ajiye mukamin da Warner yayi, kwamitin da’a ya rufe duk wani bincike akansa kuma an dauka a matsayin baida laifi”.

An dakatar da Warner ne sakamakon binciken cin hanci da rashawa akanshi.

Da Warner da Mohammed Bin Hammam an zargesu da baiwa kungiyoyin kwallon yankin Caribbean pan dubu dari shida.

Fifa ta kara da cewar “Muna takaicin yadda abubuwa suka kasance har Mr Warner yayi murabus”.

Mr Warner zai bar Fifa don kashin kanshi bayan shafe shekaru talatin a hukumar, kuma zai maida hankali wajen aiki da gwamnatin Trinidad and Tobago a matsayin Minista.

Fifa ta jinjinawa Warner saboda gudunmuwar daya bayar wajen bunkasa cigaban kwallon kafa musamman a yankin Caribbean.