Algeria ta kebe mutane biyu don nada koci

Mohamed Raouraoua Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kwallon Algeria Mohamed Raouraoua

Bayan takade da rareya, hukumar kwallon kafa ta kasar Algeria ta rage yawan masu neman zamowa kocin 'yan kwallonta zuwa biyu kacal.

Amma dai hukumar bata bayyana sunayen mutane biyun da suka samu nasara daga cikin mutane sittin da suka nuna sha'awarsu akan mukamin ba.

Sai dai rahotanni sun nuna cewar Raymond Domenech da Roger Lemerre da Raddy Antic da kuma Vahid Halilhodzic a cikinsu ne mutum daya zai samu.

Hukumar kwallon ta ce zuwa karshen watan Yuni zata sanarda sabon koci.

Kwallon kafa a Algeria yanata fuskantar koma bawa tun lokacin gasar cin kofin duniya a bara.

Kocin 'yan kwallon kasar Benchika ya yi murabus ne bayan Morocco ta casa su daci hudu da nema a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a farkon wannan watan.

Benchikha ya maye gurbin Rabah Saadane watanni tara da suka wuce.