Usmanov ya kara yawan hannun jarinsa a Arsenal

usmanov
Image caption Alisher Usmanov

Hamshakin dan kasuwa na kasar Uzbekistan Alisher Usmanov ya kara yawan hannun jarinsa a Arsenal zuwa fiye da kashi ashirin da tara cikin dari.

Wannan matakin ya biyo bayan shawarar daya yanke na kin sayarda nashi hannun jarin bayan Stan Kroenke wanda yafi kowa a Arsenal yawan hannun jari yayi kokari siye jarin kowa a kulob din a watan Afrilu.

Kamfanin Usmanov mai suna Red and White Holding a wata sanarwa yace "Red & White na sanarda cewar yanada hannun jarin fiye da kashi ashirin da tara cikin dari a Arsenal Holdings plc."

Dan kasuwan Amurka Kroenke a yanzu yana da jarin fiye da kashi sittin da shida cikin dari a Arsenal .

Usmanov ya sayi hannun jarin Arsenal a watan Agustan 2007 a lokacin daya biya mataimakin shugaban kulob din David Dein fan miliyan saba'in da biyar akan hannun jarin 14.65 cikin dari.