Kocin Porto Villas-Boas ya yi murabus

boas Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Andre Villas-Boas

Wanda Chelsea ke hari a matsayin kocinta na gaba Andre Villas-Boas ya mika takardar ajiye mukaminsa a FC Porto.

Kulob din Porto ne ya sanarda haka a wata sanarwa.

Villas-Boas mai shekaru 33 ana tunanin zai maye gurbin Carlo Ancelotti wanda aka kora a watan Mayu.

Porto ta ce Villas-Boas zai iya batin kulob din idan har aka bada fan miliyan 13 da dubu dari biyu kamar yadda yake a kwangilarshi da ita.

Villas-Boas ya jagoranci Porto ta lashe kofina uku a kakar wasan data wuce wato na gasar kwallon kasar dana FA da kuma na Europa.

Porto a kakar wasan data wuce babu kulob din daya samu galaba akanta inda suka samu nasara a karawa 27 cikin 30.

Villas-Boas ya yi aiki karkashi Jose Mourinho a Porto da Chelsea da kuma Inter Milan, sannan ya samo aiki horadda 'yan kwallo ne a kulob din Academica a shekara ta 2009.