Birmingham za ta dauki Hughton a matsayin koci

Chris Hughton
Image caption Chris Hughton tsohon kocin Newcastle ne

Ana saran Chris Hughton zai zamo sabon kocin Birmingham City bayan ya cimma yarjejeniya da kulob din domin maye gurbin da ake da shi a St Andrew's.

Tsohon kocin na Newcastle an amince da shi ne kan Roberto di Matteo domin ya maye gurbin Alex McLeish.

Rabon da Hughton ya jagoranci wani kulob tun watan Disamba lokacin da Newcastle ta kore shi.

Amma shugaban Birmingham Carson Yeung yana saran zai jagoranci kulob din zuwa gasar Premier a gwajin farko.

Hughton zai karbi kungiyar ne bayan da McLeish ya yi murabis ranar 12 ga watan Yuni inda ya tsallaka zuwa makwaftan Birmingham domin maye gurbin Gerard Houllier a Aston Villa.