Rahoton Fifa ya kama Bin Hammam da laifi

hammam Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mohammed Bin Hammam

Rahoton da Fifa ta fitar wanda kamfanin dillancin labarai na Press Association ya gani ya ce akwai hujjar dake nuna cewar Mohammed bin Hammam yayi amfani da kudi wajen kamfe na shugabancin Fifa.

Kwamitin da'ar ya kara da cewar tsohon mataimakin shugaban Fifa Jack Warner "ya taimaka wajen cin hanci".

Warner ya ajiye mukaminsa a ranar Litinin sannan ya fita daga harkar kwallon kafa baki daya.

Akan haka kuma Fifa ta dakatar da bincike akan Warner inda ta ce "tamkar baida laifi".

Amma dai rahoton kwamitin karkashin jagorancin dan Namibia Petrus Damaseb ya ce "akwai kwararan hujjojin dake nuna cewar an biya jami'ai kudi don su goyi bayan Bin Hammam a takararsa na shugabancin Fifa".

A ranar 29 ga watan Mayu aka dakatar da Warner dan kasar Trinidad and Tobago da Bin Hammam dan kasar Qatar bisa wannan zargin.

Bin Hammam daga bisani ya janye daga kalubalantar Sepp Blatter a takarar kafin ya gurfana gaban kwamitin da'a.

Bin Hammam da Warner sun musanta zargin aikata laifi.