Inter Milan ta musanta zawarcin Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Tevez

Inter Milan ta ce ba zata sayi dan kwallon Manchester City Carlos Tevez ba, sannan tayi korafin cewar yadda ake musayar 'yan kwallo a bana ya wuce misali.

A 'yan watanni da suka wuce aka yita alakanta dan kwallon Argentina mai shekaru ashirin da bakwai komawa San siro.

Amma dai darektan wasanni na Inter Marco Branca ya shaidawa Bbc cewar"Tevez babban dan kwallo ne amma dai akai kasuwa".

Branca ya kara da cewar"albashinsa ya wuce misali, kasuwar musayar 'yan kwallon ya wuce kima".

A watan Disamba ne Tevez ya rubutawa Manchester City takardar barin kulob din amma daga bisani ya janye, sai dai ana saran zai fice daga kulob din a kafin kakar wasa mai zuwa.