Chelsea ta nada Villas-Boas a matsayin koci

boas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andre Villas-Boas

An nada Andre Villas-Boas a matsayin sabon kocin Chelsea.

Tsohon kocin Porto din ya kulla yarjejeniyar shekaru uku a Stamford bridge inda yake shirya fara aiki a ranar Laraba.

Villas-Boas na shekaru guda ne da wasu 'yan wasanshi kamarsu Frank Lampard da Didier Drogba wato shekaru 33.

Sanarwar da Chelsea ta fitar ta ce "Andre ya samu mukamin, kuma ya kasance daya daga cikin matasan koci na kwallon kafa".

Chelsea ta biya pan miliyan 13.3 a matsayin diyya don Porto ta bar kocin ya tafi.

Tsohon kocin Chelsea John Hollins na ganin cewar Villas-Boas zai cimma burin nadashi da aka yi don kuwa burin mai kulob din Roman Abramovich shine lashe gasar zakarun Turai.

Amma tsohon dan wasan Chelsea Pat Nevin na ganin cewar nada Villas-Boas tamkar cacane.

Villas-Boas ya aiki a karkashin Jose Mourinho a Porto da Chelsea da kuma Inter Milan ya soma aikin koci ne tare da kulob din Academica a watan Oktoban 2009.