Grant ya gargadi Villas-Boas akan Abramovich

villas boas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andre Villas-Boas tsaran Lampard da Drogba ne

Tsohon kocin Chelsea Avram Grant ya gargadi Andre Villas-Boas cewar dole ne sai ya samu nasarori ba tare da bata lokaci ba don ya gamsarda mai kulob din Roman Abramovich.

Villas-Boas mai shekaru 33 a ranar Laraba ne aka nada shi a Chelsea bayan ya samu nasarar lashe kofina uku a Porto a shekararsa ta farko a matsayin koci.

Grant yace"Roman mutum ne dake son nasara kuma yana bada duk abinda ya dace don a samu".

Grant ya jagoranci Chelsea a kakar wasa ta 2007/08 amma sai Abramovich ya koreshi bayan sun kamalla gasar premier a matsayin na biyu sannan kuma Manchester United ta dokesu a wasan karshe na gasar zakarun Turai.

A cewarsa"na san Pep Guardiola matashin koci ne a lokacon daya fara a Barcelona kuma baida gogewa sosai, amma daga bisani yayi aiki me kyau".

Tsohon kocin Chelsea Jimmy Floyd Hasselbaink na ganin cewar bai kamata a musalta Villas-Boas da tsohon kocin Blues wato Jose Mourinho.