Dan Lens Varane zai koma Real Madrid

varane Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raphael Varane

Shugaban kungiyar Lens Gervais Martel ya tabbatar da cewa dan kwallonsa na baya Raphael Varane zai koma Real Madrid.

Varane mai shekaru 18 ya haskaka matuka a kakar wasan data wuce a kulob din Lens a Faransa.

An bayyanashi a matsayin daya daga cikin kwararrun masu tsaron baya a Turai, kuma Sir Alex Ferguson na Manchester United.

Martel ya ce Varane zai hade da Jose Mourinho a Bernabeu.

Ya kara da cewar "zai buga a Real Madrid karkashin jagorancin Jose Mourinho kuma tuni a tattauna da mai baiwa kulob din shawara Zinedine Zidane."