Young ya kulla yarjejeniyar da Manchester United

Ashley Young
Image caption Ashley Young

Ashley Young ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da Manchester United daga Aston Villa.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda dan kasar Ingila ne an siyeshi a kan fan miliyan 17.

Ya dai shafe shekaru hudu da rabi a Villa bayan da ya bar Watford, amma akwai sauran shekara guda a kwantiraginsa.

Young - wanda ya zira kwallo a wasan da Ingila ta tashi 2-2 da Switzerland - ya taka leda sau 15 a kasarsa.

Sabon kocin Aston Villa Alex McLeish ya fada a farkon makon nan cewa Young na son barin kulob din.

Villa ta sayi Young a kan fan miliyan 9 da doriya a watan Janairun shekara ta 2007 kuma ya zira kwallaye 30 a Premier.

Yanzu abinda ya ragewa Sir Alex Ferguson a Manchester United shine siyen sabon gola don maye gurbin Edwin van der Sar a yayinda ake tunanin golan Atletico Madrid David de Gea shine zai zo Old Trafford.