Ashley Young na gab da komawa Man United

Ashley Young Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Ashley Young ya buga wasanni 15 a tawagar kasar Ingila

BBC ta fahimci cewa dan wasan gefe na Aston Villa Ashley Young na kan hanyarsa ta komawa Manchester United.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda dan kasar Ingila ne za a sayeshi ne kan fan miliyan 17.

Ya dai shafe shekaru hudu da rabi a Villa bayan da ya bar Watford, amma akwai sauran shekara guda a kwantiraginsa.

Young - wanda ya zira kwallo a wasan da Ingila ta tashi 2-2 da Switzerland - ya taka leda sau 15 a kasarsa.

Sabon kocin Aston Villa Alex McLeish ya fada a farkon makon nan cewa Young na son barin kulob din.

Villa ta sayi Young a kan fan miliyan 9 da doriya a watan Janairun shekara ta 2007 kuma ya zira kwallaye 30 a Premier.