Inter ta nada Gasperini a matsayin koci

Gian Piero Gasperini Hakkin mallakar hoto inter milan
Image caption Gasperini shi ne koci na uku da Inter ta dauka cikin watanni sha biyu

Inter Milan ta sanar da nadin Gian Piero Gasperini a matsayin sabon kocin kulob din, inda zai sa hannu kan kwantiragin shekara biyu.

Bayan rade-radin da akai ta yi kan wanda kulob din zai nada, wata sanarwa a shafin intanet na kulob din ta ce:

"Gian Piero Gasperini ne sabon kocin Inter. Za a bayar da cikakkiyar sanarwa da zarar an kammala komai da komai. Daga nan ne kuma za a bayyana ranar da za a gabatar da shi ga 'yan jarida.

"Gasperini mai shekaru 53, zai sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu, inda kuma zai yi aiki tare da sabbin mataimaka biyu Bruno Caneo da Luca Trucchi."

Shugaban kulob din Massimo Moratti, ya bayyana farin cikinsa da daukar Gasperini, yana mai fatan ya jagoranci kulob din zuwa nasara a wasanni daban-daban.

Gasperini zai maye gurbin Leonardo, wanda ya karbi ragamar daga hannun Rafael Benitez a watan Disamban bara, inda ya lashe gasar Coppa Italia.