Park Ji-Sung zai ci gaba da zama a United

Park Ji-Sung
Image caption Park Ji-Sung ya taka leda sau 177 a United tun shekara ta 2005

Park Ji-Sung ya ce zai ci gaba da zama a Manchester United abin da ya kawo karshen rade-radin da ake yi kan makomarsa.

Dan wasan mai shekaru 30 a baya ya ce zai bar United idan bukatar hakan ta kama.

An kuma danganta tsohon dan wasan na Koriya ta Kudu da komawa Atletico Madrid da Savilla.

Amma yanzu dan wasan ya bayyana cewa yana son ci gaba da zama a United domin taimakawa kulob din lashe gasar League a karo na 20.

"Abin alfahari ne a gare ni in ci gaba da takawa Manchester United leda," kamar yadda ya shaidawa manema labarai a Hong Kong.

"Ba zance kala game da batun sauya kulob ba - kawai ina so na ci gaba da zama a United.

Park ya zo Manchester United ne a shekara ta 2005, kuma ya buga wasanni 177 a kulob din karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson.