CAN 2012:Za a rarraba kasashe a watan Oktoba

caf
Image caption Hukumar kwallon Afrika

A ranar 29 ga watan Oktoba ne za a rarraba yadda kasashe zasu kara da juna a gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a badi.

Masu mausakin baki wato Gabon da Equitorial Guinea su sunada gurbinsu sannan kuma Ivory Coast da Botswana sun riga sun samu gurbi biyu daga cikin 14 da suka rage.

Sauran kasashe 12 da zasu shiga gasar za a sansu kafin ranar tara ga watan Oktoba.

Abin mamaki dai Masar wacce ta lashe gasar sau shida baya akwai yiwuwar ba zata buga gasar ba saboda Afrika ta Kudu ce ke jagorantar rukunin da take.

Sai Kamaru wacce ta lashe gasar sau hudu a baya, amma a yanzu tana bin bayan Senegal a kokarin samun gurbin zuwa gasar.

Sakatare Janar na hukumar kwallon Afrika wato Caf Hicham El Amrani ya bayyana cewar za a raba kasashen goma sha shidan zuwa rukuni hudu.

Sannan kasashe biyu na farko daga kowanne rukuni zasu tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe inda za a bude gasar a ranar 21 ga watan Junairu a Malabo sannan a buga wasan karshe a Libreville a ranar 12 ga watan Fabarairu.