Ana gwada lafiyar David De Gea a United

de gea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David De Gea

Ana gwada lafiyar golan Atletico Madrid David De Gea a Manchester United a yinkurinsa na canza sheka.

Dan shekeru ashirin din zai maye gurbin Edwin van der Sar a Old Trafford kuma rahotanni sun nuna cewar za a sayeshi akan kusan fan miliyan 20.

United ta riga ta saye Phil Jones daga Blackburn da kuma Ashley Young daga Aston Villa.

De Gea na daga cikin tawagar Spain data lashe gasar matasan Turai 'yan kasada shekau 21 a ranar Asabar.

Van der Sar ya bugawa United wasanni 250 ya kuma lashe gasar premier sau hudu kafin yayi ritaya bayan wasan karshe na gasar zakarun Turai inda suka sha kashi a wajen Barcelona a watan Mayu.

A halin yanzu Ferguson nada masu tsaron gida uku wato Tomasz Kuszczak da Anders Lindegaard da kuma Ben Amos amma dai ana ganin cewar De Gea ne zai zamo lamba daya a kulob din.

Tsohon dan kwallon Manchester United Diego Forlan ya ce Ferguson ya zabi magajin Van der Sar daya dace.