Adebayor ya 'gwale' PSG da Blackburn Rovers

adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Adebayor

Dan wasan Manchester City Emmanuel Adebayor ya gwale kungiyoyin Paris Saint-Germain da Blackburn wadanda suka nuna sha'awa akansa.

City ta bada aron Adebayor zuwa Real Madrid na watanni shida a farkon wannan shekarar.

A zamansa a La Liga, Real Madrid ta lashe gasar Copa del Rey.

Adebayor ya nuna cewar yanason ya taka leda na dundun a Bernabeu amma babu tabbas Real ta shirya biyan kudin da City ke bukata akan Adebayor.

Amma dai Adebayor ya ce ba zai koma daya daga cikin wadannan kulob din saboda yanason ya lashe kofina.