De Gea ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar a United

de gea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David De Gea da Sir Alex Ferguson

Manchester United ta tabbatar da sayen sabon gola David de Gea daga Atletico Madrid a kwangilar shekaru biyar.

Golan wanda ke kamawa tawagar Spain a matakin 'yan kasada shekaru 21 ya sanya hannu kwangilar data kai akalla fan miliyan goma sha takwas da miliyan dari tara.

De Gea mai shekaru 20 ya bayyanawa gidan talabijin na kulob din Manchester wato MUTV cewar"Na yi matukar farin ciki na zaku in fara buga kwallo a nan".

Ya kara da cewar "Idan kulob mai girma kamar Manchester United tana zawarcinka, tabbas mutum zai yi murna, kuma na shirin zage damtse".

Wannan yarjejeniyar ta sanya De Gea ya zama gala na biyu mafi tsada a duniya inda yake bayan Gianluigi Buffon, wanda Juventus ta siya akan fan miliyan 32.6 a shekara ta 2001.

Jerin masu tsaron gida da suka fi tsada a tarihi:

* Gianluigi Buffon - £32.6m * David de Gea - £18.9m * Angelo Peruzzi - £10.5m * Craig Gordon - £9m * Fabien Barthez - £7.8m